<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ban Gane Yadda Zunubai na Adam Sun Rayu LW386</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ban gane yadda zunubai na Adam sun rayu
 A cikin dukan mutane babba ko ƙarami.

[V2]
 KORUS
 Amma ga shi, nan, Magana ce ta Allah
 Ta Ubangiji, na gaskanta shi.
 Na karanta shi nan, na gaskanta shi
 Ya ishe ni, ya isa.

[V3]
 2) Ban gane yadda Allahmu ya sabko duniya nan
 Ya ɗauki jikin ƴan Adam ya bar sama a can.
 Korus

[V4]
 3) Ban gane yadda Allah fa ya aza nawa laifi
 A bisa Ɗansa a giciye, nasarata ya ci.
 Korus

[V5]
 4) Ban gane yadda Allah fa ya buɗe kabari
 Yesu ya biya pansata, rai na har abada.
 Korus

[V6]
 5) Ban gane yadda jininsa ya wanke zunubi
 Ya ba ni tashi daraja, yanzu ɗansa ni ke.
 Korus.

[V7]
 6) Ban gane yadda wata rana Yesu zai fyauce ni
 Shi kai ni can wurin Uban da sauran masu bi.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>386</hymn_number>
</song>